Shugaban ofishin shugaban kasar Lebanon, Antowan Shaqir ya bayyana cewa; Shugaban kasar ya bukaci jakada Mustafa Adib da ya fara shirin kafa sabuwar gwmanati.
Adib ya ziyarci fadar “Ba’abdah’ inda ya gana shugaban kasa Micheal Auna, inda ya fadawa manema labaru cewa; Na gana da shugaban kasa Aun, ya kuma sanar da ni bukatarsa da ta ‘yan majalisa na fara shirin kafa sabuwar gwamnati,don haka ina yi masa da kuma ‘yan majalisar godiya saboda nauyin da su ka dora mani. Ina kuma rokon Alalh ya ba mu samun dacen kafa gwamnari cikin sauri.”
Adib ya kara da cewa; Yanzu ba lokaci ne na yi alkawulla ba, lokaci ne na yin aiki da hada kai da kowa da kowa domin samarwa da kasar mafita.
342/